An samo tarkacen jirgin Egypt Air

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Francoise Hollande ya ce jirnin na Egypt Air ya fadi.

Hukumomi a Masar sun ce an samu tarkacen jirgin saman kasar da ya bace a sararin samaniyar gabashin tekun Bahar Rum ranar Laraba da dare.

An tsinci wasu sassa na jirgin mallakin Egypt Air, a kan ruwa kusa da tsibirin Karpathos da ke kasar Girka.

Jirgin ya taso ne daga birnin Paris, kan hanyarsa ta zuwa Cairo, dauke da fasinjoji da ma'aikatan jirgi su 66.

Ministan sufurin kasar Masar Sherif Fathy, ya ce ya fi zaton akwai hannun 'yan ta'adda maimakon lalacewar wata na'ura a sanadin faduwar jirgin saman.

Jami'ai a Girka kuma sun ce sai da jirgin ya juya ta hannun hagu da dama kafin daga bisani ya bace a yayin da ya yi kasa.

Tun da farko dai Shugaban kasar Faransa Francoise Hollande ya bayar da tabbacin faduwar jirgin da ya taso daga Paris zuwa Alƙahira.

Tuni dai aka aika masu aikin ceto zuwa wurin da ake zaton jirgin ya ɓace.