Paparoma Francis zai gana da Limamin Al-Azkhar

Hakkin mallakar hoto epa

Fadar Vatican ta sanar da cewa Paparoma Francis zai gana da Babban Limamin masallacin jami'ar Al-Azhar, jami'ar da ta fi samun daukaka ga mabiya Sunnah.

Za a yi wannan ganawa ta tarihi a ranar Litinin a fadar ta Vatican.

Jami'ar Al-Azhar din da ke birnin Alkahira ta samu sabani da fadar Vatican a shekara ta 2011, bayan da Paparoma Benedict, mai murabus, ya yi kira da a tsaurara tsaro ga Kiristoci a Masar, bayan wani harin bam din da aka kai a cocin Alexandria.

An yi wa wannan furuci nasa kallon katsalanda a harkokin gwamnatin Masar.

Dangantaka dai sannu a hankali ta gyaru tsakani, bayan da Paparoma Francis din ya zamo shugaban fadar ta Vatican , wanda neman maslaha tsakanin addinai ke cikin abubuwa da ya sa gaba.