An halasta auren jinsi ɗaya a Seychelles

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba James Michel ne ya bukaci a sauya dokar.

Gwamnatin kasar Seychelles ta halasta auren jinsi daya.

Kamfanin dillancin labaran kasar ya ce majalisar dokokin kasar ce ta yi gyara ga dokar da ta haramta auren jinsi daya a kasar, wacce ake amfani da ita tun lokacin turawan mulkin mallaka.

Dokar dai ta bukaci a yi wa masu auren jinsi daya daurin shekara 14.

Sai dai shugabannin Coci-coci na kasar sun soki matakin da majalisar ta dauka.

A watan Fabrairu ne dai shugaban kasar ta Seychelles James Michel ya ce yana so a halasta auren jinsi daya a kasar.