Ana fuskantar barazana daga kwayoyin cuta

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Wasu na ganin ba a yi bincike sosai kan miyagun kwayoyin cutar ba.

Wani rahoto ya nuna cewa miyagun kwayoyin cutar bakteriya za su rika kashe mutum daya a duk dakika uku nan da shekarar 2050 muddin duniya ba ta dauki matakin gaggawa ba.

Rahoton ya bayar da shawarar a sake fasalin yin riga-kafi ta hanyar kashe biliyoyin dala domin shawo kan kwayoyin cutar.

Ya kara da cewa akwai bukatar fito da sabbin hanyoyin amfani da magunguna, sannan a wayar da kan jama'a kan yadda za su yi amfani da su.

Sai dai wadanda suka fitar da rahoton na shan suka, inda wasu ke ganin ba a yi bincike sosai kan miyagun kwayoyin cutar ba.