An gano sassan jikin fasinjan EgyptAir

Tawagar dake neman sassan jirgin Egyptair da ya yi hatsari sun gano sassan jikin waɗanda suke cikin jirgin da ya ɓace ranar Alhamis.

Masu aikin ceton sun kuma gano kayayyakin wasu fasinjan jirgin da kuma kujerun jirgin.

A 'yan awoyin da suka gabata bayanai sun nuna cewa, wutar dake nuna cewar, hayaƙi na fitowa daga wani sashen na jirgin ta kama kafin jirgin ya ɓace ɗauke da mutane 66.

Wakilin BBC kan harkokin tsaro ya ce, wannan na nuna cewa, kodai hatsari ne ya auku, ko kuma wani abu ya fashe, amma ba za a tabbatar da abunda ya faru ba sai an samu na'urar naɗar bayanan jirgin.

A can birnin Alƙahira dangin waɗanda lamarin ya rutsa da su sun yi addu'oi a masallatai.