Hakar zinariya ba bisa ka'ida ba a Ghana

Masu hakar zinariya ba bisa ka'ida ba a kasar Ghana, sun soma rubibin mamaye filayen hakar zinariya.

Daga cikin filayen da suka mamaye har da na wasu kamfanonin hakar zinariyar kasar.

Sun kuma kai hari kan akalla mahakan zinariya uku na kasar.

Wannan barazana ta sa an fara nuna damuwa a kasar ta Ghana.