France: An yi wa Ginola tiyata a zuciya

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ginola bai yi nasara ba kan kudirinsa na zama shugaban hukumar Fifa a 2015

Tsohon dan wasan gaba na Faransa, David Ginola, yana farfadowa daga dashen jijiyoyi hudu da aka yi masa a zuciyarsa, a asibitin Monaco.

Dan wasan, mai shekara 49 wanda ya yi ritaya a 2002, ya faɗi a kudancin Faransa, ranar Alhamis.

A ta bakin likitan da ya yi wa Ginola tiyata, Var-Matin ya ce an kwartan da dan wasan ne a wani "mummunan yanayi."

David Ginola ya fara shahara ne a gasar wasan kwallon Ingila, bayan da ya koma kulob din Newcastle a 1995. Ya kuma bugawa Tottenham da Aston Villa da kuma Everton, wasa.