An zargi ɗan sandan Biritaniya da cin-hanci

Hakkin mallakar hoto Getty

An zargi hukumar masu shigar da kara ta Biritaniya da yin rufa-rufa kan cin-hancin da ake zargin 'yan sanda sun yi, bayan an samu wasu sabbin hujjoji game da shari'ar dan siyasan nan na Najeriya, James Ibori.

Hukumar dai ta amsa laifin cewa tana da wasu bayanan sirri da ke tabbatar da zargin da ke cewa wani jami'in rundunar 'yan sandan Biritaniya, watau Scotland Yard, ya amshi cin hanci domin kwarmata bayanan sirri game da shari'ar James Ibori a shekarar 2007.

Da farko dai masu shigar da karar sun musanta wannan zargi, inda suka ki bayar da bayanai da ke tabbatar da laifin da dan sandan ya aikata.

Labarin dai ya yi sanadin cire jami'in, mai suna John McDonald, daga aikinsa a sashen yaki da almundahana na kasashen waje, a hukumar yaki da laifuffuka ta kasa, watau National Crime Agency.

'Yan sandan Biritaniya dai sun tabbatar da cewa an soma bincike game da matsayin dan sandan.

Labarin yadda aka kame James Ibori a London a shekarar 1990 har ya zamo gwamna a kasar sa Najeriya, daga bisani kuma ya sake komawa gidan kaso a Biritaniya na da ban mamaki kwarai.

A shekarar 2005 'yan sandan Biritaniya ta soma sanya masa idanu, bayan sun gano wani jirgi da ya saya ta hannun wani lauyasa da ke London.

A shekarar 2007 kuma an zargi Ibori da sakin makudaden kudade wajen yakin neman zabe marigayi Yar'Adua , duk da cewar ya musanta hakan.

Lauyoyinsa dai sun kare shi, inda suka ce da ma can ya Ibori dan kasuwa ne kuma tun kafin aikin gwamnati yana da nasa dukiyar.