Tsananin zafi ya halaka jama'a a India

Hakkin mallakar hoto

An shiga wani tsananin yanayin zafin da ba'a taba kaiwa ba a jihar Rajasthan na kasar Indiya, inda ya kai har 51ga ma'aunin Celsius.

Yanzu haka tsananin zafin da ake yi a duk fadin Indiya ya hallaka gwamman mutane, kazalika a Delhi an samu karuwar bugun zuciya.

Wakilin BBC ya ce an fadawa mutane su zauna a gida, wadanda ke aiki kuma da suka hada da magina da 'yan sanda, a basu ruwan gishiri da siga a matsayin wani matakin kariya.

Duk da tsananin zafin da ake yi a India, a makociyar ta Larkana kuwa a kasar Pakistan yanayin ya haura na indiya da maki daya, inda ya kai maki 52 a ma'aunin Celcius.

Yanzu haka an kafa daruruwa cibiyoyin bada agaji a birnin Karachi dake gabar ruwa, domin taimakawa mutanen da tsananin zafin ka iya shafa.