An gano sassan jikin fasinjojin Egypt Air

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iyalan mutanen da ke cikin jirgin sun yi matukar kaduwa.

Masu binciken jirgin nan mallakin Egypt Air da ya yi hadari a tekun Bahar Rum, sun gano sassan jikin Pasinjojin jirgin.

Jami'an Masar sun ce ma'aikatan Sojin ruwa sun kuma gano wasu daga cikin kayan mutanen.

Hotunan tauraron dan Adam sun nuna wani bangare na tekun Bahar Rum da wani abu da ya yi kama da malalar Mai.

Dan uwan Ayman Dawood mai suna Wifki ya na cikin jirgin da ya bace, ya shaidawa BBC cewa su na bukatar karin bayani kan lamarin

Yace ya rasa dan uwansa, wanda ke da yara biyu, mace da namiji, da ke zaune a Faransa da iyalan nasa

Ya kara da cewa ya kamata hukumomi su basu karin bayani, idan da hali su ba su gawarwakin 'yan uwan na su.

Tun da farko dai Rundunar sojin Masar ta ce an gano tarkacen EgyptAir wanda ya da ya fada tekun Bahar Rum ranar Alhamis.

Kasashen Girka da Masar da Faransa da kuma rundunar sojin Biritaniya ne suka kaddamar da gagarumin bincike a kusa da tsibirin Karpathos da ke Girka domin yiwuwar gano jirgin.

Jirgin, mai lamba MS804, ya tashi ne daga Paris zuwa birnin Alkahira na kasar Masar dauke da fasinja 66 da kuma ma'aikatansa a lokacin da ya yi layar-zana.

Kasar Girka ta ce bayanan da ke nuna tafiyar jirgin, sun nuna cewa jirgin samfurin Airbus A320, ya yi ta jujjuyawa sannan ya fada a teku.

Masar ta ce mai yiwuwa 'yan ta'adda ne suka harbo jirgin, ba wai matsalar na'ura ba.