Cutar Zika ta bullo a Africa

Hakkin mallakar hoto Roger Eritja

A karo na farko, Hukumar lafiya ta Duniya -- WHO, ta tabbatar da bullar kwayar cutar Zika a Afrika, cutar da ake alakantawa da haihuwar dubban 'ya'ya gilu a nahiyar Amurka.

WHO ta ce gwaje-gwaje da aka gudanar sun nuna alamun cutar Zika a tsibirin Cape Verde da ke a yankin tekun yammacin Afrika, an kuma gane cewa kwayar cutar iri daya ce da ta Amurka.

Ana kyautata zaton cutar da sauro ke janyowa na janyo lahani ga jarirai, musamman a kwakwalwarsu, idan masu ciki sun kamu da shi.

Jami'an lafiya sun ce mata 157 da ke da juna biyu a Amurka yanzu haka na dauke da cutar ta Zika.