Ma'aikata na zanga-zanga a Bauchi

Gwamnan Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar. Hakkin mallakar hoto Bauchi State Govt
Image caption Ma'aikatan sun yi yajin aiki ne saboda kin biyansu albashin watanni biyar.

Dubban ma'aikata na zanga-zanga birnin Bauchi a arewacin Nijeriya domin nuna rashin jin dadinsu kan rashin biyansu albashi na kimanin watanni biyar.

Ma'aikatan dauke da kwalaye da ganye sun yi tattaki zuwa gidan gwamnatin jihar suna zargin gwamnatin jihar da yaudararsu bayan da ta sha yi masu alkawarin biyansu albashin.

An dai samu tsaiko wajen biyan albashin ne sakamakon aikin tantance ma'aikatan da gwamnati jihar ta kwashe watanni tana gudanarwa domin fitar da ma'aikatan boge.

Amma ma'aikata da dama wadanda aka tantance su aka kuma tabbatar da su na hakika ne, ba a biya su ba, lamarin da ya harzuka ma'aikatan.

To sai dai mukaddashin shugaban ma'aikata na jihar Bauchi, Alhaji Liman Bello, wanda ya yi wa ma'aikatan jawabi a madadin gwamnan jihar, ya rarrashi ma'aikatan yana mai cewa gwamnati ta janye aikin tantancewar, kuma ya yi masu alkawarin cewa za a biya su albashin nan da makwanni biyu.