Jami'yyar PDP ta sauke Ali Modu Shariff

Jamiyyar PDP ta sauke Sanata Ali Modu Shariff daga shugabancinta ta kuma nada tsohon gwamnan jihar Kaduna Sanata Ahmed Makarfi a matsayin shugaban riko.

Jamiyyar tayi wannan nadin ne a babban taronta da ya gudana yau a birnin Fatakwal na jihar Ribas.

Sabon shugaban na wucin gadi zai tafiyar harkokin jam'iyyar na tsawon watani biyu kafin ta gudanar da babban taronta.

A waje guda kuma wani bangare na jamiyyar shi ma ya gudanar da nasa taron a birnin Abuja inda ya nada sanata Ibrahim Mantu a matsayin shugaban jamiyyar ta PDP.