Bankin Duniya zai taimakawa talakawa

Bankin Duniya Hakkin mallakar hoto
Image caption Za a bada kudaden ne dan yaki da cututtuka a kasashe matalauta.

Bankin Duniya ya sanar da zai bada tallafin gaggawa na kudi Dala miliyan dari biyar dan yaki da cututtuka a duniya.

Bankin zai yi aikin hadin gwiwa da hukumar lafiya ta duniya WHO, za a bada tallafi ga kasashe matalauta da kuma kungiyoyin kasashe dan yaki da cututtukan da suka addabi al'uma.

Shugaban bankin Jim Yong Kim, ya shaidawa BBC cewa sabon shirin maida martani zai yi akan yadda kasashe suke tafiyar hawainiya dan tallafawa yaki da ake da cutar Ebola.

Wadda ya ce ba matsalar kasa daya ko yankin Afurka ba ce kadai, ta shafi duniya baki daya.