Anfani da Internat na karuwa ga masu shekaru sama da 75

A kalla kashi 2 cikin 3 na matanan da ke da shekaru sama da 75 a Birtaniya basu anfani da shafin zamani na internat ba.

Wani bincike da hukumar kididiga ta gudanar a Birtaniya ya sanar da hakan.

To kuma sai dai duk da hakan, yawan masu anfani da shafin internat na kokarin linkawa su biyu tun 2011.

An gano da cewa, kashi 25 cikin dari na jama'ar da ke da nakasa na anfani da internat.

Kimanin kashi 88 cikin 100 na dukan tsofafin Birtaniya su milyan 46 sun yi anfani da internat a cikin watanni 3 na baya-bayanan.