India da Iran za su kulla dangantakar tattalin arziki

Hakkin mallakar hoto Reuters

Firayim Ministan Indiya, Nerandra Modi ya isa Iran don yin ziyara, a karon farko cikin sama da shekara goma da suka wuce.

Mista Nerandra Modi dai ya kai ziyarar ne da nufin kyautata huldar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu, ganin cewa na dage wa kasar Iran din takunkumin tattalin arziki.

Iran sun samu cikas a mu'amalar da suke yi da juna ne lokacin aka kakaba wa Iran takunkumin karya tattalin arziki, amma yanzu Mista Modi ya zaku wajen ganin sun kulla wata sabuwar hulda.

Ana sa ran tattaunawar da za su yi da shugaban Iran, Hassan Rouhani za ta tabo shirin Iran din na bunkasa tashar jirgin ruwanta da ke Chabahar a kuduncin kasar.

Indiya dai na da niyyar zuba jari a wannan harkar, wadda za ta bunkasa kasuwanci tsakaninta da Iran din da kuma Afghanistan.

Ana sa ran cewa shugaban Afghanistan, Ashraf Ghani shi ma zai isa Iran din a yau Litinin domin sanya hannu a kan wata yarjejeniya da ta shafi kasashe ukun.