Ruwa ya zama gwal a Indiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Firai Minista Modi ya yi kira ga 'yan aksar su yi tattalin ruwa

Firai ministan Indiya Narendra Modi, ya yi kira ga 'yan kasar da su guji almubazzaranci da ruwa ko da digo daya ne, sakamakon halin da kasar ke ciki na matsananncin fari, wanda tsananin zafi ya jawo.

Da yake jawabi ga 'yan kasar ta gidan rediyo, Mista Modi ya bayyana ruwa a matsayin wata kyauta mai kamar gwal daga wajen Ubangiji.

Gomman mutane ne suka rasa rayukansu sakamakon tsananin zafin da ake fama da shi.

Kwanaki biyu da suka gabata ne Indiya ta sanar da yanayin zafin da ya kai maki 51 na ma'aunin selshiyas da ba a taba samun irinsa ba, a jihar Rajasthan.

Wasu masu suka sun zargi hukumomi da munana lamarin saboda gazawarsu wajen shawo kan matsalolin rashin ruwa.india water

Karin bayani