Iraq: Ana yunkurin kwato birnin Fallujah

Hakkin mallakar hoto AFP

Firayim Ministan Iraqi, Haider al-Abadi ya ba da sanarwar wata gagarumar arangamar da soji ke yi domin kwace birnin Fallujah daga hannun mayakan IS wadanda suka cinye shi shekaru biyun da suka wuce.

Firayim Ministan ya yi jawabi ne ta gidan Talabijin, yana cewa nan ba da dadewa ba tutar Iraki za ta fara kadawa a birnin Fallujah mai tazarar kilomita 50 daga Bagadaza.

An dai tura karin sojoji da 'yan sanda don yi wa birnin kawanya.

Tuni dai mahukunta a Iraki suka gargadi mazauna birnin, wadanda galibinsu iyalan mayakan IS ne da su fice daga birnin.