'Yan sanda sun mamaye hedikwatar PDP

Image caption Rikicin jam'iyyar PDP ya ki ci ya ki cinyewa

Jami'an tsaro sun mamaye hedikwatar jam'iyyar adawa ta PDP a Nigeria, a ranar Lahadi.

Duk da cewa ba a samu tabbacin dalilin yin hakan ba, an alakanta daukar wannan mataki da riga-kafi don kaucewa barkewar rikici saboda dambarwar da ke faruwa a jam'iyyar kan shugabanci.

Mai magana da yawun Sanata Ali Modu Sheriff, Inuwa Bwala, ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin, amma ya ce ba su samu wani bayani daga rundunar 'yan sanda ba.

Sai dai ya ce, ''Hakan ba zai rasa nasaba da takaddmar da ke faruwa a jam'iyyar kan shugabanci ba, saboda gudun barkewar rikici.''

Mista Bwala ya ce 'ya'yan jam'iyyar za su bi doka da oda, duk da cewa ba su san har zuwa yaushe jami'an tsaron za su kasance a wajen ba.

Tun a ranar Asabar ne aka fara samun sabani kan karbar shugabancin riko na jam'iyyar adawar, inda a yanzu haka mutane uku ke ikirarin su ne shugabanninta.