Za a fara taro a kan ayyukan jin kai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram ta raba miliyoyin mutane daga muhallansu.

A ranar Litinin ne ake fara wani taron koli kan halin da 'yan gudun hijira ke ciki a duniya.

Taron na kwanaki biyu -- wanda za a yi a birnin Santambul na kasar Turkiyya -- zai duba hanyoyin inganta yadda ake ba da agaji da kuma yadda kasashen duniya za su ba da gudummawa dan tallafawa 'yan gudun hijira.

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa Najeriya ce kasa ta biyar da ta fi kowacce yawan 'yan gudun hijira a bara sakamakon rikicin Boko Haram.

Wannan ne dai karon farko da za a yi babban taro irin sa domin bunkasa tare da inganta ayyukan jin kai ga 'yan gudun hijrar kasashen da rikice-rikice suka tagayyara tare da kuma magance halin kuncin da 'yan gudun hijrar ke ciki.

Kididdigar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi a bara ta nuna cewa mutane fiye da miliyan sittin ne suka rasa matsugunnansu a fadin duniya a kasashen da suke fama da rikice-rikice.

Kasar Yemen ita ce ta farko a yawan 'yan gudun hijrar, sai kuma Syria da ta biye mata,sai Iraqi da Ukraine sannan kuma Najeriya ta biyar inji majalisar dinkin duniya.