Libya ta kama kwale-kwalen 'yan gudun hijira

'Yan gudun hijira na yawan bi ta Libya domin shiga Turai

Asalin hoton,

Bayanan hoto,

'Yan gudun hijira na yawan bi ta Libya domin shiga Turai

Masu tsaron gabar tekun Libya sun ce sun kama wasu kwale-kwale dauke da 'yan gudun hijira 850 da ke kokarin isa Turai a ranar Lahadi.

Wani babban jami'i ya ce 'yan gudun hijirar wadanda suka fito daga kasashen Afrika daban-daban sun hada da mata 79 kuma 11 daga cikinsu masu ciki ne, an kuma same su a wasu kananan kwale-kwale kusa da Sabratha, da ke yammacin Tripoli babban birnin kasar.

Fiye da 'yan gudun hijira 30,000 ne suka samu damar tsallake Libya zuwa Italiya a wannan shekarar.

Wannan al'amari na zuwa ne daidai lokacin da ake taron Majalisar Dinkin Duniya kan ayyukan jin kai a birnin Istanbul na Turkiyya.