Microsoft zai hana yada ta`addanci ta intanet

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption kamfanin microsoft ya ce wajibi ne a hana yaduwar ta`addanci

Kamfanin Microsoft ya sanar da wani sabon tsari na hana yada bayanan da suka shafi ta'addanci ta kafofinsa na intanet.

Kamfanin ya ce zai haramta wallafa duk wani bayanin da ya shafi harkar ta'addanci ko kungiyoyin 'yan ta'adda, ko kuma bayanan da za su iya ingiza mutane shiga wannan harkar.

Wannan mataki zai shafi shafukansa na intanet da suka hada da Xbox Live da Outlook webmail.

Sai dai kamfanin ya bayyana cewa matakin ba zai hana amfani da kuran-bayanai wajen zuko bayanan da suka shafi ta'addanci idan bukatar hakan ta taso ba, matukar doka ba ta hana yin haka ba.

A cewar kamfanin, ya kamata al'umomi da gwamnatoci su iya rarrabewa tsakanin 'yancin fadar albarkacin baki da linzamin da za a iya sanyawa ga wasu bayanai.

Kazalika kamfanin ya ce zai kwadaita wa masu amfani da shafukansa su dinga ankarar da shi a duk lokacin da aka sanya bayanan da suka shafi ta'addanci a shafukansa, kodayake kamfanin ya ce yana kokarin yin na'urar da za ta iya sansanar bayanai masu alaka da ta'addanci, har ma da hotuna da kuma bidiyo.

Ya ce yayin da ake samar wa jama'a sukunin wadata kai da bayanai, bai kamata a taimaka wa al'uma wajen yin aika-aika ko miyagun ayyuka ba.