Buhari: Shin kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yaki da kungiyar Boko Haram na cikin manyan alkawuran da Buhari ya yi wa 'yan Najeriya.

A ranar 29 ga watan Mayu ne shugaban Najeriya Muhamadu Buhari yake cika shekara ɗaya da hawa ragamar mulki bayan ya kayar da Goodluck Jonathan a zabe mafi zafi da aka fafata a ƙasar. Shin kwalliyar ta fara biyan kuɗin sabulu?

Shugaba Buhari, wanda 'yan kasar ke yi wa lakabi mai gaskiya, ya lashe zaben shekarar 2015 bayan ya sha kaye sau uku a yunkurinsa na zama shugaban Najeriya.

A lokutan da yake yakin neman zabe, Shugaba Buhari ya mayar da hankali a kan batutuwa uku: samar da tsaro, yaki da cin hanci da rashawa da kuma samar da ayyukan yi ta hanyar bunaksa tattalin arzikin Najeriya.

Shekara guda bayan ya hau mulki, shin za a iya cewa kwalliya ta fara biyan kudin sabulu?

'Tabbatar da tsaro'

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Buhari ya nemi agajin makwabtan kasashe domin murkushe Boko Haram.

A lokacin da Muhammadu Buhari ya karbi mulkin Najeriya, kasar na tsaka da yaki da kungiyar Boko Haram, wacce ta kashe dubban mutane, kana ta raba da miliyoyinsu daga gidajensu, musamman a yankin arewa maso gabashin kasar.

A lokacin, kungiyar ta kwace garuruwa da dama, bayan ta kori mutanen da ke cikinsu, sannan ta kafa daular da ta kira "Daular Musulinci."

Dakarun sojin Najeriya sun kara kaimi wajen fatattakar 'yan kungiyar, inda suka kwato kusan daukacin garuruwan da ke hannun 'yan Boko Haram, sannan suka kashe 'yan kungiyar tare da kama wasunsu.

Kazalika, sojojin na Najeriya, tare da hadin gwiwar sojojin kasashen da ke kusa da tafkin Chadi, sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin sun kawar da abin da kakakin runduanr sojin kasa ta Najeriya, Kanar Sani Usman Kukasheka, ya kira "gyauron 'yan ta'adda" daga yankunan.

Hakan ya faru ne bayan da Shugaba Buhari ya rika ziyarar kasashen da ke makwabtaka da Najeriya -- Nijar da Kamaru da Chadi da kuma Benin -- domin samun hadin kansu kan yadda za a murkushe 'yan Boko Haram.

Baya da wannan, Shugaban na Najeriya ya bukaci agajin kasashe mambobin G7, cikin su har da Amurka, domin kakkabe 'yan Boko Haram, lamarin da ya sa a baya bayan nan kasar ta Amurka ta yi alkawarin sayarwa Najeriya jiragen yaki domin kai wa 'yan Boko Haram farmaki.

Sai dai a yayin da hakan ke faruwa, wani batun tsaro da ke ci gaba da ci wa Shugaba Buhari tuwo a kwarya shi ne yadda har yanzu ba a ceto 'yan matan makarantar Chibok 219 da 'yan Boko Haram suka sace ba a watan Afrilun shekarar 2014.

Image caption A kwanakin baya ne aka ceto daya daga cikin 'yan matan Chibok.

Shugaban ya sha yin alwashin ceto su, kuma ko da a makon jiya sai da sojojin kasar tare da hadin gwiwar 'yan kato-da-gora suka ceto daya daga cikinsu.

'Yaki da cin hanci'

Masu sharhi a kasar dai suna ganin baya ga yunkurin tabbatar da tsaro babu abin da Shugaba Muhammadu Buhari ya fi taka rawar gani kamar yaki da masu cin hanci da rashawa.

Jim kadan bayan hawansa kan mulki, Shugaba Buhari ya fara gudanar da bincike kan yadda aka kashe kimanin $2.1bn da aka ware domin sayen makaman yaki da 'yan Boko Haram.

Hakan dai ya kai ga kama Kanar Sambo Dasuki, tsohon mai bai wa tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan shawara kan sha'anin tsaro.

Hukumar EFCC, wacce ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, ta zargi Kanar Dasuki da yin amfani da kudin wajen yakin neman zaben tsohon shugaba Jonathan, zargin da ya sha musantawa.

Image caption An gurfanar da Kanar Sambo Dasuki a gaban kotu bisa zargin sace $2.1bn.

Hakan dai ya sa an kama mutane da dama, wadanda ake zargi an bai wa wani bangare na kudin.

Kazalika, EFCC tana zargin tsohuwar ministar man fetur, Diezani Allison-Madueke da sace makudan kudade a lokacin da take mulki.

EFCC ta kwace gwala-gwalai da wasu kayayaki na Misis Madueke, wacce yanzu haka take birnin London inda take jiyya.

Baya ga ita, hukumar ta kama wasu makusantanta da kuma wasu jami'an gwamnatin da ta gabata bisa zargin cin hanci.

Shugaba Buhari ya kuma nemi hadin kan kasashen duniya, cikin su har da Biritaniya da Amurka da Hadaddiyar Daular Larabawa, domin dawo wa Najeriya kudaden da ake zargi wasu 'yan kasar sun sace sun kuma boye a kasashen.

Haka kuma shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Bukola Saraki, yana gaba kotu domin wanke kansa bisa zargin yin karya wajen bayyana kadarorinsa, ko da ya ke shi ma ya sha musanta zargin. Wasu na ganin hakan yana cikin matakan da Shugaba Buhari ya dauki na yaki da cin hanci ba tare da sani ko sabo ba, duk da cewa wasu na ganin hakan a matsayin siyasa.

Wasu masu sharhi na ganin akwai bukatar yin gyara ga dokokin yaki da cin hanci da rashawa na kasar idan Najeriya na son kawo karshen matsalar ta cin hanci da rashawa.

'Tattalin arziki'

A bangaren tattalin arziki, masana na ganin Shugaba Buhari ya taka sahun barawo.Sun bayyana haka ne kuwa ganin yadda farashin man fetur, wanda shi ne babban abin da Najeriya ke sayarwa a duniya, ya yi mummunar faduwa.

Gabanin zamansa shugaban kasar, ana sayar da kowacce gangar fetur a kan fiye da $100, amma tun da Shugaba Buhari ya zama shugaban kasa farashin gangar mai ya koma kasa da $50.

Baya ga haka, Shugaba Buhari ya ce a lokacin da ya karbi mulki, kusan babu ko sisi a asusun kasar, yana mai zargin cewa jami'an gwamnatin da ta gabata sun kusa durkusar da Najeriya.

Image caption Gwamnatin Buhari ta kara farashin fetur daga N86.90 zuwa N145.

Sai dai tsohuwar gwamnatin ta musanta zargin.

Wasu dai na dora alhakin tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya da kuma mawuyacin halin da 'yan kasar ke ciki kan Shugaba Buhari, suna masu cewa har yanzu ba shi da tsayayyun masu ba shi shawara kan tattalin arziki, shi ya sa ya rasa yadda zai shawo kan matsalar.

Sai dai shugaban ya ce ya dauki matakai domin bunkasa tattalin arzikin da hana sata, ciki har da tabbatar da cewa kowacce ma'aikatar gwamnati ta sanya kudin da take samu a asusun gwamnatin tarayya da korar ma'aikatan bogi da rage irin facakar da jami'an gwamnati ke yi.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Darajar Naira na ci gaba da faduwa.

'Yan kasar da dama dai na ganin wani dalili na kasa yin katabus din shugaba Buhari kan tattalin arziki shi ne rashin nada ministoci da wuri, wadanda su ne za su ja ragamar ma'aikatun kasar.

Haka kuma, ko da ya ke gwamnatin kasar ta kara farashin man fetur daga N86.50 zuwa N145 lamarin da ya sa kungiyar kwadagon kasar ta shiga yajin aiki, gwamnatin ta ce ta ware fiye da N500bn domin rage radadin da cire farashin zai yi.

Masana dai na ganin akwai jan aiki a gaban shugaba Buhari a yunkurin da yake yi na bunkasa tattalin arzikin kasar, ganin irin mawuyacin halin da take ciki da kuma yadda kusan kacokan ta dogara ga man fetur.