Za a janye wa Vietnam takunkumin makamai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An kashe miliyoyin 'yan Vietnam a lokacin yakin.

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayar da sanarwar cewa za a janye takunkumin hana sayarwa Vietnam makamai.

A baya dai Vietnam babbar abokiyar gabar Amurka ce.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin ziyarar da yake yi a kasar, yana mai cewa ya dasuki matakin ne "domin kawo karshen yakin cacar-bakin da kasashen boyu suka kwashe tsawon lokaci suna yi".

Mista Obama ya ce bangarorin biyu sun amince da juna don haka za su yi aiki tare

Shugaban na Amurka na yin ziyarar ne 41 bayan gama yakin Vietnam, lokacin da Amurka ta nemi a hana Vietnam mamaye Kudancin Vietnam.

An kashe miliyoyin 'yan kasar ta Vietnam - cikin su har da fararen hula da mayakan jam'iyyar Kwaminist civilians, da sojojin kudancin Vietnam - da kuma sojin Amurka kusan 58,000 a lokacin yakin.