'Yan Boko Haram na kwarara Kano

Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta bukaci mazauna birnin su rika kula da abubuwan da ke faruwa a yankunansu saboda 'yan kungiyar Boko Haram na kwarara cikin birnin.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Maigari Abbati Dikko, ya shaida wa wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai cewa, hakan na faruwa ne sakamakon fatattakar 'yan kungiyar da dakarun sojin kasar ke yi daga dajin Sambisa na jihar Borno.

Ya bukaci mutane su kai rahoton duk wata bakuwar fuska da ba su amince da ita ba ga rundunar 'yan sanda.

Kwamishinan ya yi karin bayanin ne bayan an kama wata mata da ta ce 'yan Boko Haram sun sanya mata bama-bamai a jikinta, kana suka umarce ta da ta tayar da su a kasuwar Kantin Kurmi da ke birnin na Kano:

Ku saurari karin bayanin nasa anan:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti