An daina yin Coca Cola a Venezuela

Karancin sukari da wutar lantarki a kasar Venezuela sun tursasa wa kamfanin Coca Cola ya daina yin lemon sha.

An bayyana haka bayan babban kamfanin da ke yin lemon kwalaba na kasar, Empresas Polar, ya daina aiki sakamakon rashin isasshiyar wutar lantarki.

Coca Cola ya ce za a dakatar da masu raba lemon na matsakaicin zango sakamakon rashin kayayyakin yin Coca Colar.

Wani mai magana da yawun kamafinin na Coca cola ya ce, kamfanin zai ci gaba da yin lemo maras sukari kamar irinsu coca cola maras sukari wanda ake kira (diet coke) da turanci.

Ya kara da cewa "Za mu hada kai da gwamnati da kuma abokan kasuwancinsu domin shawo kan matsalar cikin gaggawa".

Tattalin arzikin kasar Venezuela dai ya tabarbare saboda faduwar farashin man fetur.