Eritrea ta cika shekara 25 da samun 'yanci

Image caption Ana bikin ne ta hanyar maci a titunan da ke Asmara.

Kasar Eritriya na bikin cikarta shekara 25 da samun 'yancin kai daga kasar Habasha ko Ethiopia.

Ana bikin ne ta hanyar maci a titunan da ke Asmara, babban birnin kasar, inda ake kada badujala da masu raye-rayen gargajiya na rausayawa, ga kuma sahun wasu mutane da suka yi shiga irin ta sojojin 'yan tawayen kasar, wadanda suka shefi shekara talatin suna fadan kwatar 'yanci.

Mutanen kasar da ke neman tafiya kasahen Turai sun fi na sauran kasashen Afirka yawa, ga kuma sukar da ake yi wa mahukuntan kasar cewa suna take hakkokin bil'adama.

Kuma dubban 'yan kasar da kasashen waje sun yi turuwa gida domin halartar bikin.