Kishirwa ta kashe mutum 8 a Niger

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jiragen sojin Amurka ne suka gano gawarwakin a Sahara

An gano gawarwakin wasu mutane takwas a arewacin Arlit kusa da iyakar Aljeriya a Jamhuriyar Nijar.

An tarar da gawarwakin mutanen ne dab da motarsu, kuma ana kyautata zaton kishirwa ce ta kashesu, bayan da motar ta lalace.

Wani jirgin sojin Amurka da ke shawagi a sararin samaniyar hamadar yankin ne ya gano gawarwakin mutanen.

Daga nan sai suka sanar da sojojin Nijar da sansaninsu ke da nisan kilomita 50 da wajen.