Mafarauta na fuskantar kalubale a kudancin Najeriya

Hakkin mallakar hoto AP

Tun fiye da shekaru goma da suka gabata, mafarautan arewacin Najeriya suke zuwa dazuzzukan kudancin kasar, dauke da bindigogi kirar adaka da adduna da gatura da wukake da sauransu, suna gudanar da sana'arsu ta farauta.

To, sai dai a 'yan shekarun nan mafarautan suna fuskantar wasu matsaloli a dazuzzukan na kudu da aka fi sani da kurmi.

Yanzu haka dai mafarautan na taka sahun barawo a dazuzzukan lamarin da ke kaisu zama a gidan kaso.

To ko me yakamata mafarautan suyi domin kaucewa shiga wata matsala? Alh Badamasi Saleh, shi ne shugaban 'yan arewa mazauna jihar Edo ya shaidawa BBC cewa, yakamata kafin mafarautan su zo sai wasu daga cikinsu su zo ba wai dan suyi farauta ba sai su samu shugabannin al'ummar yankunan da suke so su shiga domin farauta, hakan zai sa a hada su da kungiyar mafarautan yankunan hakan zai sa ba zasu matsala ba saboda an san ko su waye.

Tun shigowar rikicin boko haram a arewacin Najeriya da kuma yawan sace-sacen mutane domin neman kudin fansa galibi a kudancin kasar, mafarautan suka fara fuskantar wannan kalubale.