Tsutsa ta tagayyara manoma tumatur a Nigeria

Image caption A baya dai manoma sun rika shanya tumatur domin gudun yin asararsa.

Manoman rani a Nigeria sun ce sun fuskanci mummunar asarar tumatur sakamakon wata tsutsa da take cinye tumatur din a lokacin da yake gona.

Matsalar dai ta haifar da karancin tumatur da kuma tsadar sa a Nigeria, inda yanzu kwando daya ya kai dubban Nairori.