Rikicin PDP ya gwara kan kotuna

Image caption Hukunce-hukuncen kotuna ya kara dagwala rikicin PDP

A Najeriya, hukunce-hukunce da kotuna biyu masu daraja daya suka yanke a kan rikicin shugabancin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP sun kara ruda al'amarin.

A ranar Talata ne dai wata babbar kotu a jihar Lagos ta sauke Sanata Ahmad Makarfi daga shugabancin riko na jam'iyyar PDP, inda ta bayar da umarnin mayar da Sanata Ali Modu Sheriff kan mukamin shugaba.

Kazalika wata babbar kotu a Fatakwal ta yanke hukuncin da ya dakatar da Senata Ali Modu Sherif din daga shugabancin jam'iyyar zuwa lokacin da za ta kammala sauraron wata karar da aka kai mata.

Wadannan hukunce-hukunce masu karo da juna dai sun daure kan jama'a inda wasu ke tambayar ko wane hukunci za a dauka a tsakanin biyun.

Barrister, Baba Dala Hassan Lauya ne mai zaman kansa a Abuja, kuma Ibrahim Isa ya tambaye shi ta waya, don jin yadda yake kallon lamarin ta mahangar shara'a ga kuma bayanin da ya yi:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti