Haibatullah ne sabon shugaban Taliban

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan dai shi ne karon farko ta kungiyar ta fito fili ta ce an halaka Mullah Mansour.

Kungiyar Taliban ta nada sabon shugaba mai suna Maulawi Haibatullah Akhundzada.

Sabon shugaban ya maye gurbin Mullah Akhtar Mansour, wanda jirage marasa matuka na Amurka suka hallaka a makon jiya.

Da ma dai Mullah Haibatullah shi ne mataimakin Mullah Akhtar Mansour, kuma shi ne shugaban ma'aikatar shara'a ta Taliban.

Kazalika kungiyar ta nada Sirajuddin Haqqani da Mohammad Yaqoob, wato dan wanda ya kafa kungiyar Taliban, Mullah Omar a matsayin mataimakan sabon shugaban.

Wannan dai shi ne karon farko ta kungiyar ta fito fili ta ce an halaka Mullah Mansour.