Rundunar Afirka na gab da fara aiki

Herve Ladsous ya ce fara aikin rundunar na da muhimmanci.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Herve Ladsous ya ce fara aikin rundunar na da muhimmanci.

Jami'in da ke kula da ayyukan wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya, Herve Ladsous ya ce ya ji dadin cewa rundunar ko-ta-kwana ta Tarayyar Afirka na gab da fara aiki.

Herve Ladsous ya shaida wa kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya cewa, fara aikin rundunar Tarayyar Afirkan na da muhimmanci, kasancewar a halin da ake ciki rundunoni tara ne a Afirka, daga cikin rundunonin wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya guda 16.

Tun shekaru 20 din da suka wuce aka kuduri aniyar kafa rundunar, don haka za ta taimaka gaya wajen kai daukin gaggawa, tare da hadin-gwiwa da majalisar dinkin duniya, idan rikici ya barke a nahiyar Afirka.