Al-Qaeda ta dauki alhakin harin Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar AQIM ta ce burin ta shi ne ta hana masu "kutse" sakat.

Kungiyar Al-Qaeda da ke yankin Sahara ta ce mayakanta ne suka kai hare-haren rokoki a kamfanin ma'adinin uranium na Faransa da ke Jamhuriyar Nijar.

Kungiyar ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare a kan kamfanonin da ta ce "suna yin kutse domin kwace arzikinmu."

Wata sanarwa da kungiyar ta AQIM ta fitar ta ce mayakan Al-Nasr Brigade da ke da alaka da ita ne suka kai hari kan kamfanin Areva a garin Arlit da ke arewacin Nijar duk kuwa da matakan tsaron da aka dauka domin kare shi daga hare-hare.

A shekarar 2013 ma, kungiyar ta dauki nauyin harin kunar-bakin-wake da aka kai a kamfanin.

A watan Maris din da ya gabata ma, AQIM ta ce mayakanta ne suka kai hari a wata masana'antar iskar gas da ke Algeria ta kamfanin mai na BP, tana mai cewa hakan "wani bangare ne na yakin da take yi da masu yin kutse."