Somali ta gargadi Kenya kan 'yan hijira

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan Somalia kimanin 300,000 ke samu mafaka a sansanin Dadaab.

Shugaban Somalia Hassan Sheik Mohamed ya gargadi kasar Kenya game da korar 'yan kasarsa daga sansanin 'yan gudun hijira na Dabaab da karfin tuwo.

Ita dai Kenya ta ce tana shirin rufe sansanin, wanda 'yan Somalia 300,000 ke samu mafaka a cikinsa.

Sai dai shugaban na Somalia ya bukaci a samar da hanya mafi sauki ta fitar da 'yan kasarsa daga Kenya.

Kenya dai ta dage cewa za ta rufe sansanin ko ana ha-maza-ha-mata saboda fargabar tsaro, tana mai cewa ana kitsa yawancin hare-haren da ake kai wa a kasar ne daga sansanin na Dadaab.