Niger ta musanta ikirarin Al-Qaeda

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Al-Qaeda ta ce ita ta kai hari wurin hakar Uranium

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun musunta labarin harin da kungiyar Al-Qaeda ta ce ta kai a ranar Talata, a wani wurin hakar Uranium na kamfanin Areva da ke Arlit a arewacin kasar.

Gwamnatin ta Nijar ta karyata labarin ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta fitar.

Ta ce labarin bashi da tushe balle makama, saboda babu wani hari da aka kai wajen hakar Uranium din.

Ga rahoton Baro Arzika daga Yamai:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti