Nigeria ta bankado ma'aikatan bogi 43,000

Hakkin mallakar hoto
Image caption Binciken ya kai ga samun rarae biliyoyin naira a asusun gwamnati

Gwamnatin Najeriya ta ce ya zuwa yanzu, ta bankado ma'aikatan bogi dubu 43,000 a tsarin biyan albashin kasar.

Shugaban kwamitin da gwamnatin ta kafa domin bincike a kan albashin ma'aikata, Muhammad Kyari Dikwa, ne ya bayyana hakan.

Ya ce binciken ya kai ga samun rarar kudi na naira biliyan 50 a asusun gwamnati.

Ga rahoton Raliya Zubairu kan batun:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti