Aikin Hajji zai bunkasa tattalin arzikin Saudiya

A yayin da gwamnatin Saudiyya ta sanar da sauye-sauye da nufin rage dogaro a kan man fetur, wata hanyar da ake ganin za ta samar wa kasar kudin ta kuma bunkasa tattalin arzikinta ita ce ziyarar mahajjata.

Hukumomin kasar suna shirin saukaka takunkumi a kan bizar da ake bai wa mahajjata, kuma hakan na nufin wadanda zasu ziyarci Makkah da Madina zasu iya kara kwanaki kuma har ma su ziyarci wasu wuraren da ba na ibada ba.

Kiyasin bunkasar tattalin arziki

Bangaren yawon bude ido a kasar Saudiya na samar da kashi 2.7 cikin 100 na ma'aunin karfin tattalin arzikin kasar, kuma mutane masu zuwa aikin Hajji sune mutane mafi yawa da suke kai ziyara kasar.

A watan Dhul-Hijja Musulmai ke kai ziyara birnin Makkah domin yin aikin Hajji, sannan kuma a cikin shekara Musulmai da dama kan je Umrah, wanda hakan ke samar da dala biliyan 12 ga kasar a duk shekara.

Hukumar da ke kula da tattalin arziki da cigaban kasar ta yi kiyasin alkaluman zasu karu zuwa dala biliyan 20 duk shekara, nan da shekaru hudu masu zuwa.

Hukumar ta yi hasashen cewar yawan Musulumai da suke zuwa Umrah zai karu daga mutane miliyan takwas a wannan shekarar zuwa mutane miliyan 15 a shekarar 2020, da kuma mutane miliyan 30 zuwa shekarar 2030.

Ya zuwa yanzu dai, kasar na tsaurara matakan bayar da biza ta wajen saka takunkunmi a kan inda masu shiga kasar zasu iya zuwa da inda ba za su iya shiga ba, amma jami'ai suna fatan saukaka wadannan takunkumin.

Yarima Sultan bin Salman, shi ne shugaban hukumar da ke kula da bangaren yawon bude ido na kasar, kuma ya ce, "Muna kokari domin a bai wa mahajjata damar zuwa yawon bude ido a wurare kamar Madain Saleh da ke kusa da Madina bayan sun kammala aikin Hajji."

Arzikin da ba'a ci gajiyarsa ba

Kasar na aikace-aikace da dama a kan abubuwan more rayuwa kamar su layin dogo daga Makkah zuwa Madina da Jidda da ma wasu manyan cibiyoyi a birane.

A cikin abubuwan yawon bude ido da kasar ta tanada, har ma da abubuwan tarihi da aka tono daga karkashin kasa, wadanda suka hada da wasu duwatsu.

Farfesa Micheal Petraglia na jami'ar Oxford, wanda ke jagorantar tawagar masu binciken tarihi a karkashin kasa a Saudiyya, ya ce akwai irin wuraren da dama wadanda suka hada da Jubbah da Shuwaymis da kuma Nejran wadanda za su iya jan hankulan baki da dama.

Akwai wurare hudu na hukumar kula da al'adu na Majalisar Dinkin Duniya a Saudiyyar kuma ana duba wasu da dama a cewarsa.

Mohammad Hafez, mamba ne na hukumar kula da al'adu ta Saudiyya, kuma ya ce inganta ala'adu ya bunkasa tattalin arzikin kasar.

Hafez ya ce, "Wasu abubuwan sun kawo koma baya kan manufarmu ta ilmantar da 'yan Saudiya batun al'adu."

Wani shiri da aka sanar na yin gada a kan Bahar Maliya da za ta hada Saudiyya da Masar zai iya kara yawan zuwan baki kasar.

Wannan hanya za ta bai wa al'ummar Masar damar kara tururuwar zuwa aikin ibada fiye da baya.