Soyayya ta jawo rikicin addini a Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mafi yawan al'ummar Masar musulmai ne amma akwai kiristoci kibdawa

Rahotanni daga Masar na cewa an kona gidaje da dama a wani rikicin addini mai akala da soyayya a wani kauye da ke kudancin birnin Al-Kahira.

An fara rigimar sakamakon jita-jitar da ta fara yaduwa cewa soyayya ta kullu tsakanin wani kirista Bakibde da wata Musulma.

An kona gidajen Kiristoci tare da muzanta uwar mutumin, sannan kuma an kona gidajen Musulmai ma a kauyen.

An shafe kwanaki ana rikicin amma ba a samu cikakken bayani ba sai a yanzu.