Ghana: Shirin samarwa mabukata abinci

Image caption Za a dinga bai wa mabukata abinci kyauta

Wata kungiya mai zaman kanta a kasar Ghana, wato Food for all Ghana, ta kaddamar da wani shiri na bayar da abinci kyauta ga dubban mutanen da ba su da abinci ko kuma basu da karfin ciyar da kansu.

Kungiyar dai ta ce za ta yi anfani ne da abincin da galibi ake zubarwa a gidaje da wuraren cin abinci wajen ciyar da wadanan mutane.

Ana sanya ran hakan zai kawo karshen dabi'ar zubar da abinci da mutane suke yi.

Iddi Ali ya halarci bikin kaddamar da shirin, ga kuma rahoton da ya aiko mana:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti