Iraqi:Fararen hula na wahala a Falluja

Fararen hula kalilan din da suka iya tserewa daga birnin Falluja na kasar Iraqi da aka yiwa kawanya sun bayyana halin kuncin da suka shiga a can.

Mutane kusan dubu hamsin ne suka makale a can, yayinda dakarun gwamnati ke shirin kai farmaki don same kwato yankun daga hannun mayakan IS.

Iyalan da suka fada cikin kuncin, sun shaidawa hukumar lura da 'yan gudun hijira ta kasar Norway cewa sun cika da fargabar yunwa za ta hallaka su muddin basu samu hanyar tserewa ba.

Mai magana da yawun rundunar sojin Iraqi ya ce, sojoji a shirye suke wajen komawa fagen daga don fafatwa kai tsate da mayakan na IS.