Farashin man fetur ya tashi

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Wutar-dajin da ta tashi a Canada ta sa an rage yawan man da ake sayarwa Amurka.

Farashin fetur ya tashi zuwa $50 kan gangar danyen mai daya a karon farko a shekarar 2016 saboda yawaitar bukatarsa a kasashen duniya.

An sayar da danyen mai samfurin Brent a kan $50.07 a kasuwannin nahiyar Asiya.

Hakan ya faru ne sakamakon wasu alkaluma da Amurka ta fitar ranar Alhamis da ke nuna cewa yawan man da take samu ya ragu saboda wutar-dajin da ta tashi a kasar Canada.

Canada ce kasar da ta fi sayarwa Amurka fetur kuma wutar-dajin da ta tashi a yammacin kasar ta tilasta mata rage yawan man da take fitarwa da kimanin ganga miliyan daya a kullum.

Kazalika tattaunwar da ake yi tsakanin kungiyar kasashen da ke fitar da mai da kuma Rasha a kan ta rage yawan man da take samarwa ta taimaka wajen tashin farashin man.