Trump ya yi godiya ga magoya bayansa

Hakkin mallakar hoto EPA AFP
Image caption Alamu na nuna cewa Trump da Misis Clinton ne za su fafata a zaben neman shugabancin Amurka

Donald Trump ya yi godiya ga magoya bayansa bayan ya samu isasshen goyan bayan wakilan jam'iyyar Republican don zama dan takara.

Kamfanin dillancin labarai na AP da NBC News sun lissafa cewa Donald Trump ya samu goyan bayan wakilai 1,238, zuwa babban taron da za'a yi a watan Yuli, inda ake amincewa dan takara.

Mista Trump ya samu yawan goyan bayan wasu 'yan wakilan da ba wani alkawari a kansu.

Biloniyan dan kasuwar wanda bai taba rike wani mukamin gwamnati ba ya kada 'yan takara na jam'iyyar republican 16.