Obama na Ziyara a Hiroshima

Hakkin mallakar hoto AP

Shugaban Amurka Barack Obama na yin ziyara a Hiroshima, a karon farko da wani shugaban kasar ke kai ziyara a birnin tun bayan harin da Amurka ta kai masa a shekarar 1945.

Mista Obama ya sauka a sansanin sojin ruwan Amurka da ke Iwakuni, bayan kammala taron kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a duniya, wato G7.

Ya ce ziyararsa wata alama ce da ke nuna cewa duk gabar da ke tsakanin mutane ko kasashe, wataran za su yi sulhu.

Sai dai Mista Obama ya ce ba zai nemi gafara kan harin da Amurka ta kai a birnin ba.

Kimanin mutane 140,000 ne suka mutu sakamakon harin da Amurka ta kai da makamin nukiliya a watan Agustan shekarar 1945.

Kwana biyu bayan hakan, Amurka ta sake kai hari a birnin Nagasaki lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 74,000.