Za a yi wa Nawaz Sharif aiki a zuciyarsa

Hakkin mallakar hoto AFP

Kafofin yaɗa labaran Pakistan sun ce, cikin makon gobe ne za a yi wa Frayi ministan kasar fiɗar zuciya a wani asibitin London.

Yanzu haka dai Nawaz Sharif yana London inda aka yi masa gwaje-gwaje na lafiya.

'Yar sa ta rubuta a shafinta na Twitter cewa, za a yi wa mahafinta aiki a zuciyarsa ranar Talata mai zuwa, kuma ta nemi a yi masa addu'ar samun sauƙi.

Frayi ministan na Pakistan yana fuskantar matsin lamba daga jam'iyyun adawa bayan tonon sililin Panama Papers ya bankaɗo cewa, iyalansa suna da dukiya da suka ɓoye a ƙetare.

Aikin da za a yiwa Nawaz Sharif aiki ne da ya ƙunshi buɗe ƙirji har a kai ga zuciya inda za a yi aiki akan jijiyoyi da kuma magudanan jini.