Masassarar tsuntsaye ta dawo Cameroon

Hakkin mallakar hoto no
Image caption Shugaban Kamaru, Paul Biya

Hukumomi a kasar Kamaru sun tabbatar da samun kwayar cutar H1N1, mai haddasa masassarar tsuntsaye, a babban birnin kasar, Younde.

Ministan ma'aikatar kula da dabbobin kasar,Dr Taiga tare da na ma'aikatar lafiya, Andre Mama ne suka bayar da sanarwar barkewar cutar a yankin da gonakin kiwon kaji suke na Mvog-Betsi da ke birnin.

Kafafen yada labaran kasar sun ce kawo yanzu an kwantar da mutum daya a asibiti sannan kuma kaji dubu 15 sun mutu.

Yanzu haka gwamnatin kasar ta bayar da umarnin kashe kaji kimanin dubu 20 da ke gonar da cutar ta shafa sannan kuma a killace yankin babu shiga babu fita.

Sai dai kuma ministocin sun ce tuni gwamnati ta fara daukar matakan kariya daga bazuwar cutar, a inda suka ce mutane za su iya ci gaba da cin naman kaji ba tare da wata fargaba.

Wannan dai shi ne karon farko da kwayar cutar ta H1N1 ta waiwayi kasar tun bayan barkewar cutar a shekarar 2018.