Real Madrid sun zama zakarun Turai

Hakkin mallakar hoto Getty

Kulob ɗin Real Madrid ya lashe gasar zakarun Turai a karawar da suka yi da Atletico Madrid.

Cristiano Ronaldo ne dai ya zura ƙwallo a raga da ta baiwa Real Madrid nasara yayin bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Kafin nan dai wasan ya kasance kunnen doki tsakanin manyan kulob din na Spaniya.

Wannan dai shi ne karo na goma sha daya da Real Madrid ya lashe wannan kofi na zakarun Turai.