Za a fara yi wa jakuna kunzugu a Kenya

Amalanken jaki
Image caption Hukumomin na son kare martabar sabuwar kwaltar da aka yi ne a garin Wajir.

An haramta wa jakuna shiga garin Wajir da ke arewa maso gabashin Kenya matukar ba a musu kunguzu ba.

Hukumomin yankin sun ce an bullo da dokar ce don kare sabuwar kwaltar da aka shinfida wa titin Wajir mai amalanken jakuna birjik.

Wata sanarwa ta fada wa masu amalanken jakuna cewa sai sun rika kula da dabbobinsu don hana su sukurkuta kashi a kan kwalta wanda ke sanya kyankwami.

BBC ta lura da yadda masu amalanken jakuna ke kokarin yin aiki da wannan sabuwar doka, har ma wasu sun fara musayar shawarwari ta kafofin sada zumunta kan yadda ake yi wa jaki kunzugu.

Ko a shekara ta 2007 ma, hukumomi a garin Limuru mai nisan kilomita 50 arewa maso yammacin Nairobi babban birnin kasar, sun fitar da irin wannan umarni, ko da yake, ya gaza yin aiki.

Hukumomin garin Wajir mai nisan fiye da kilomita 600 daga Nairobi, na haba-haba wajen kare sabuwar kwaltar da aka shimfida bayan tsawon shekara gommai babu irin wannan ci gaba.