Nigeria: Mun sake fasa bututan mai — NDA

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kungiyar Niger Delta Avengers tana neman gurgunta tattalin arzikin Najeriya da kuma kokarin ballewa.

Kungiyar mayakan sa-kai ta Niger Delta Avengers ta yi ikrarin sake fasa wasu bututan mai da na iskar gas, a yankin na Niger Delta, mai arzikin mai da ke kudancin Najeriya.

Kungiyar dai ta yi ikrarin kai hare-haren, ta shafinta na Twitter, da safiyar Asabar, a inda ta ce ta fasa bututai guda uku da suka hada tashar fitar da mai ta Brass da Bonny, a jihar Delta.

Ga Usman Minjibir da karin bayani.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti