Nijeriya: Shekara ɗaya da mulkin Buhari

Hakkin mallakar hoto State House

A ranar 29 da watan Mayun bara ne, shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin zababben shugaban kasar.

Zaɓen ya ja hankalin duniya saboda irin halin da Najeriyar ta shiga na ƙalubalen tsaro, da kuma yadda hare-haren Boko Haram suka kusan durƙusar da kasar.

Najeriya ta samu kanta cikin matsalar rashin wutar lantarki, da rashin aikin yi, da kuma rikicin addini da ƙabilanci da ya karu a tsakanin 'yan kasar, da kuma matsalar cin-hanci da rashawa.

Tun a lokacin yakin neman zaben sa, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ta nanata cewa matsalar taɓarɓarewar tsaro na daga cikin muhimman batutuwan da gwamnatin sa za ta ba muhimmanci.

Sai dai wasu na ganin duk da irin nasarorin da jami'an tsaro ke cewa suna samu a kan 'yan Boko Haram tamkar baya ba zane ne, saboda a bangare guda matsalar satar mutane ana garkuwa da su da kuma hare-hare a kan bututan mai na yin kamari.

Wani batu kuma da yanzu ake ci gaba da nuna damuwa a ciki da wajen Najeriya shi ne mummunan yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

A jawabin rantsar da shugaba Buharin a bara ne dai ya ce gwamnatinsa za ta rika daukar matakai domin farfado da tattalin arzikin kasar.